Lokutan 8 da Najeriya ta fuskanci juyin mulki
1. Juyin mulki na farko – Janairu 15, 1966
Jagoran juyin mulki: Major Chukwuma Nzeogwu.
Ya hambarar da gwamnatin farar hula ta Sir Abubakar Tafawa Balewa.
An kashe manyan shugabanni da dama.
Maj. Gen. Johnson Aguiyi-Ironsi ya zama shugaban ƙasa.
2. Juyin mulki na biyu – Yuli 29, 1966
Jagoran juyin mulki: Lt. Col. Murtala Mohammed da Lt. Col. Yakubu Gowon.
An kashe Ironsi.
Gowon ya zama shugaban ƙasa.
3. Juyin mulki na uku – Yuli 29, 1975
An hambarar da Gowon yayin da yake taro a Kampala, dake ƙasar Uganda.
Jagoran juyin mulki: Col. Joseph Garba.
Murtala Mohammed ya hau mulki.
4. Juyin mulki na hudu – Fabrairu 13, 1976
Jagoran juyin mulki: Lt. Col. Buka Suka Dimka.
An kashe Murtala Mohammed.
Olusegun Obasanjo ya hau mulki a matsayin shugaban ƙasa.
5. Juyin mulki na biyar – Disamba 31, 1983
Jagoran juyin mulki: Maj. Gen. Muhammadu Buhari.
Ya hambarar da gwamnatin farar hula ta Shehu Shagari.
6. Juyin mulki na shida – Agusta 27, 1985
Jagoran juyin mulki: Maj. Gen. Ibrahim Badamasi Babangida (IBB).
Ya hambarar da Buhari.
7. Yunkurin Juyin mulki na bakwai – Afirilu 22, 1990.
Jagoran juyin mulki: Maj. Gideon Orkar.
Sun yi ƙoƙarin hambarar da Babangida, amma juyin mulkin bai yi nasara ba.
8. Juyin mulki na takwas – Nuwamba 17, 1993
Jagoran juyin mulki: Gen. Sani Abacha.
Ya hambarar da gwamnatin rikon kwarya ta Ernest Shonekan.