Kungiyar ƙwadago ta bawa gwamnatin tarayya wa’adi a kan yajin aikin ASUU

0
11
NLC
NLC

Kungiyar Kwadago ta ƙasa (NLC) ta baiwa Gwamnatin Tarayya wa’adin makonni hudu domin kammala tattaunawar da take yi da ƙungiyoyin ma’aikata a sashen ilimin gaba da sakandire.

Shugaban NLC, Joe Ajaero, ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja bayan ganawa da ƙungiyoyin da ke cikin jami’o’i, kwalejoji da kuma polytechnic.

Ajaero ya ce wannan mataki ya biyo bayan gajiyawar da ƙungiyar ta yi da rashin cika yarjejeniyoyi da kuma ƙarancin kuɗin da ake warewa ga sashen ilimi, abin da ke haddasa yawan yajin aiki a makarantun gwamnati.

Ya gargadi gwamnati da cewa idan ba ta ɗauki mataki cikin makonni hudu ba, NLC za ta jagoranci matakin gama-gari na ƙasa wanda zai haɗa dukkan ma’aikata da ƙungiyoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here