Kotun Majistire mai lamba 7 da ke Kano, karkashin jagorancin Mai Shari’a Halima Wali, ta bayar da umarni ga Rundunar Hisbah ta jihar Kano da ta jagoranci gudanar da aure tsakanin Ashiru Mai Wushirya da Basira Yar Guda Daya, a cikin kwanaki 60.
Kotun ta kuma umurci shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Kano da ya kasance mai sa ido kan yadda za a aiwatar da auren tare da tabbatar da bin umarnin kotu.
Mai Shari’a Halima Wali ta gargadi ɓangarorin cewa idan ba a kammala auren cikin wa’adin da aka bayar ba, za a sake gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa rashin bin doka.
Tun da farko dai an kama Mai wushirya tare da gurfanar da shi, bisa zargin yaɗa fitsara tare da Ƴar Guda, a kafafen sada zumunta.