Jami’ai sun tsaurara tsaro a hanyoyin shiga Abuja

0
63

Jami’ai sun tsaurara tsaro a hanyoyin shiga Abuja

Rundunar sojin da ke tsaron shugaban ƙasa tare da ’yan sanda sun kafa shingayen bincike a manyan hanyoyin da ake yin amfani da su wajen shiga birnin tarayya Abuja, sakamakon zanga-zangar da ake gudanarwa don neman a sako jagoran ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.

Wannan mataki ya biyo bayan rahotannin da ke cewa ana zargin wasu manyan sojoji da shirin juyin mulki tare da wani tsohon gwamna, lamarin da ya sanya hukumomin tsaro kara sa ido a babban birnin. Duk da cewa Hedikwatar Tsaro ta ƙaryata zargin, majiyoyi sun tabbatar da cewa bincike na ci gaba gudana kan zargin shirya juyin mulkin.

A safiyar Litinin, jagoran tafiyar #RevolutionNow, Omoyele Sowore, ya jagoranci zanga-zangar a sassa daban-daban na Abuja, abin da ya haddasa cunkoson ababen hawa a wurare irin su Bwari, Zuba, Nyanya da War College da ke Ushafa.

An rufe wasu hanyoyi da ke haɗa Bwari da tsakiyar birnin, abin da ya jawo wahalar zirga-zirga ga ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a.

Majiyoyi daga hukumomin tsaro sun bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin hana masu tayar da fitina ko ’yan kutse shiga cikin birnin, tare da tabbatar da tsaron cibiyoyin gwamnati.

“Yanzu ana binciken kowace mota da ke shigowa birnin domin tabbatar da cewa babu masu shirin tada tarzoma,” in ji wani jami’in tsaro.

Wasu direbobi da fasinjoji sun koka kan tsaikon da aka samu, inda suka ce tsauraran matakan sun jawo cunkoson ababen hawa mai tsanani, musamman a yankin Nyanya da Ushafa.

A halin da ake ciki, jami’an tsaro sun ci gaba da sa ido a manyan wurare da suka haɗa da Fadar Shugaban Kasa, Majalisar Tarayya, Kotun Daukaka Kara da Eagle Square, domin tabbatar da zaman lafiya a Abuja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here