Gwamnatocin Kano, Jigawa da Katsina zasu inganta samar da lantarki a jihohin su

0
46

Gwamnatocin Kano, Katsina da Jigawa sun kulla yarjejeniyar haɗin gwiwa domin bunƙasa kasuwancin wutar lantarki a jihohin su tare da zuba hannun jari a kamfanin makamashi na Future Energies Africa (FEA), wanda shi ne babban mai zuba jari a kamfanin rarraba lantarki Kano KEDCO.

Wannan bayani na cikin wata sanarwa da Kwamishinan Wutar Lantarki da Makamashi na Jihar Kano, Dr. Gaddafi Sani Shehu, ya fitar.

A cewar sanarwar, an cimma yarjejeniyar ne yayin taron bunƙasa harkar lantarki da aka gudanar a Marrakech, Morocco, daga 16 zuwa 19 ga Oktoba, 2025.

Dr. Gaddafi ya bayyana cewa jihohin za su hada kai wajen inganta kasuwannin wutar lantarki da samar da dokoki da tsare-tsaren hadin gwiwa domin ƙarfafa aiki. Ya ce wannan mataki zai taimaka wajen ƙarfafa dabarun KEDCO da kuma haɓaka samar da lantarki a yankin Arewa maso yamma.

Kwamishinan ya kara da cewa za a kafa asusun naira biliyan 50 domin hanzarta samar da wuta ta hanyoyi daban-daban, ciki har da hasken rana da tsarin samar da wuta a gida.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here