Yawan Al’umma Na Iya Tsananta Matsalar Tsaro a Nijeriya–Bankin Duniya

0
8

Bankin Duniya ya yi gargadi cewa karuwar yawan jama’a a Nijeriya na iya haifar da karin matsaloli musamman a fannin tsaro da tattalin arziki. 

Rahoton bankin ya nuna cewa idan ba a dauki matakan da suka dace ba wajen  samar da ayyukan yi, inganta ilimi da walwalar jama’a, to kasar na iya fuskantar karin rikice-rikice da rashin zaman lafiya a nan gaba.

Bankin ya kuma jaddada bukatar gwamnati ta zuba jari sosai wajen bunkasa noma, kiwon lafiya da ilimi domin rage tasirin karuwar jama’a ga tsaron kasa da ci gaban tattalin arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here