Uba Sani ya bayyana yadda al’ummar Kaduna zasu zaɓi APC a shekarar 2027

0
9

Gwamna Uba Sani, ya ce Jihar Kaduna za ta bai wa jam’iyyar APC kashi 95% na kuri’u a zaɓen 2027.

Uba Sani, ya bayyana haka ne a wani gangamin APC da aka gudanar a Murtala Square, dake Kaduna, inda wasu ‘yan majalisar jiha da na tarayya suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar.

Sani ya ce wannan karɓuwa ta biyo bayan adalci da haɗin kan da gwamnatinsa ke aiwatarwa, yana mai cewa babu rikicin addini ko kabilanci tun bayan da suka hau mulki.

Ya tabbatar wa sabbin mambobin APC cewa za a ɗauke su daidai da tsofaffin mambobi, yayin da manyan jiga-jigai na jam’iyyar suka yaba da nasarorin gwamnan da Tinubu.

Tsohon gwamnan Kaduna Muktar Ramalan Yero, da tsofaffin sanatoci Shehu Sani, Danjuma Lah, da Hunkuyi na daga cikin wadanda suka sauya sheƙa zuwa APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here