Dole ne dalibai su ci jarrabawar lissafi kafin kammala Sakandire—Gwamnatin tarayya

0
7
Tinubu
Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa daga yanzu, kowane ɗalibi na sakandare dole ne ya ci jarabawar Lissafi (Mathematics) kafin ya kammala karatunsa.

Ministan Ilimi, Dr. Maruf Olatunji Alausa, ya bayyana hakan yayin wani taro da shugabannin ma’aikatar ilimi a Abuja. Ya ce matakin zai taimaka wajen inganta ƙwarewar ɗalibai a fannin kimiyya da fasaha.

Ya ƙara da cewa Lissafi na da matuƙar muhimmanci wajen ci gaban tattalin arziki da kuma shirya ɗalibai domin shiga fannonin da suka shafi fasaha, injiniya da tattalin arziki.

Gwamnatin ta kuma ce za ta ƙara saka hannun jari wajen horas da malamai da samar da kayan koyarwa domin tabbatar da ɗalibai suna samun ingantaccen ilimi a wannan fanni.

Ministan ya ƙara da cewa:

Ministan yace ba za mu iya gina ƙasa mai ƙarfi ba idan matasanmu ba su da tushe mai ƙarfi a Lissafi da Kimiyya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here