Ƴan sanda sun gargaɗi masu zanga-zanga a kan zuwa fadar shugaban ƙasa

0
13

Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta yi gargaɗi ga masu niyyar gudanar da zanga-zanga domin neman a saki jagoran IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, da su guji kusantar fadar shugaban ƙasa Aso Rock.

CSP Benjamin Hundeyin, mai magana da yawun ‘yan sanda, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, wannan gargaɗi na bin umarnin kotun tarayya da ta bayar a ranar 17 ga Oktoba 2025, wacce ta hana duk wata zanga-zanga a yankin Villa da wuraren da ke kusa da ita.

Wuraren da aka haramta gudanar da zanga-zanga sun haɗa da:

Aso Rock Villa

Majalisar Tarayya

Hedikwatar ‘Yan Sanda

Kotun Daukaka Kara

Eagle Square

Hanyar Shehu Shagari

Hundeyin ya ce duk wanda ya karya wannan doka ko ya yi amfani da zanga-zanga wajen tayar da tarzoma, daukar makami ko lalata dukiyar jama’a, za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kuliya bisa dokokin laifuka da na ta’addanci.

Ya kara da cewa rundunar ‘yan sanda ta tanadi tsaro mai ƙarfi domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, tare da tabbatar da zaman lafiya a Abuja.

Ya kuma shawarci masu zanga-zangar su bi hanyoyin doka wajen bayyana korafe-korafensu maimakon yin fito-na-fito da gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here