Tinubu ya dawo Abuja bayan taron yaki da ta’addanci a Rome
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dawo Abuja bayan halartar taron shugabannin ƙasashe na Aqaba Process da aka gudanar a birnin Rome, Italiya.
Taron ya haɗa manyan shugabannin duniya domin ƙarfafa haɗin kai wajen yaƙi da ta’addanci da kuma tsattsauran ra’ayi.
Tinubu ya bar Najeriya ne a ranar 12 ga Oktoba domin halartar taron da aka fara a ranar 14 ga watan.
A cewar sanarwar da mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Asabar, tace tafiyar ta shugaban ƙasa ta sake tabbatar da jajircewar Najeriya wajen ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a duniya baki ɗaya.
An bayyana cewa Aqaba Process wani shiri ne da Sarki Abdullah II na Jordan ya ƙaddamar a 2015 domin haɗa kan ƙasashe wajen yaƙar ta’addanci. Taron na Rome ya mayar da hankali ne kan ƙarfafa haɗin kai tsakanin ƙasashe musamman a yammacin Afirka wajen shawo kan matsalar ta’addanci da tsattsauran ra’ayi.