Hedkwatar Tsaron ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta kan cewa an yi yunkurin juyin mulki a ƙasar nan ba gaskiya ba ne.
A cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X a ranar Asabar, DHQ ta ce rahoton da ke danganta soke shagulgulan bikin cikar Najeriya shekara 65 da samun ’yanci da yunkurin juyin mulki karya ne kuma makirci ne na tada hankalin jama’a.
DHQ ta kara da cewa binciken da ake yi kan sojoji 16 ba ya da nasaba da siyasa ko wani yunkuri, illa dai mataki na cikin gida domin tabbatar da ladabi da da’a a cikin rundunar soji.
“An kafa kwamitin bincike wanda zai kammala aikinsa, sannan za a fitar da sakamakon a bainar jama’a,” in ji sanarwar.
DHQ ta roki ’yan Najeriya da su guji yada labaran karya, tare da tabbatar da cewa rundunar soji na ci gaba da aiki tukuru wajen kare hadin kan kasa da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.