Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta nuna damuwa kan matakin Saudiyya na rage wa Najeriya adadin kujerun aikin Hajji zuwa 66,910 a shekarar 2026.
Kakakin hukumar, Fatima Sanda Usara, ta ce an rage kujerun ne saboda Najeriya ta kasa cike kujeru 95,000 da aka ware mata a 2025, inda aka bar 35,872 babu masu zuwa.
Ta gargadi cewa matakin zai hana mutane da dama yin Hajji, yayin da wasu ‘yan ƙasa ke danganta matsalar da tsadar kuɗin Hajji.
A halin yanzu, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya umarci hukumar da ta rage farashin aikin Hajji na 2026 domin sauƙaƙa wa maniyyata.