Mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, ya kai ziyarar aiki a kasar China domin jawo hankalin masu zuba jari a bangaren makamashi da tsaro.
A yayin ziyarar, an karɓe shi cikin girmamawa a manyan kamfanonin kasar, ciki har da POWERCHINA Huadong da Dahua Technology, wadanda suka nuna shirin yin hadin gwiwa da gwamnatin Kano domin samar da ingantaccen tsaro da makamashi.
Ziyarar ta biyo bayan irin ta da Sarki Sanusi II ya yi a Amurka da Tunisiya, da nufin kara bunkasa tattalin arziki da ci gaban masana’antu a jihar Kano da Najeriya baki ɗaya.
A ranar 15 ga Oktoba, 2025, Sarkin ya halarci taron injiniyoyi na duniya (WFEO) a Shanghai, inda ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin kasashe wajen habaka fasaha da makamashi a nahiyar Afrika.
Mai bawa Sarkin shawara kan harkokin noma, Malam Ahmad Husain, ya bayyana cewa kamfanonin China sun nuna niyyar haÉ—in kai da gwamnatin Kano don inganta samar da wutar lantarki a jihar.
Masarautar Kano ta ce wannan ziyara za ta taimaka wajen karfafa tsaro, samar da ayyukan yi, da bunkasa tattalin arzikin jihar.