Gwamnatin Jihar Kano ta karɓe lasisin mallakar gidajen da ba a ci gaba da gina su ba a unguwannin Kwankwasiyya da Amana, bayan cikar wa’adin watanni biyar da aka bayar domin masu gidajen su fara ko su ci gaba da aikin gini a wajen.
Kwamishinan Ma’aikatar Bunkasa Gidaje ta jihar, Arch. Ibrahim Yakubu Adamu Wudil, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka gudanar a ranar Alhamis, 16 ga Oktoba, 2025, a dakin taro na sabuwar ma’aikatar dake Kundila.
Ya ce gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf ta ɗauki wannan mataki ne bayan cikar wa’adin da aka bayar, inda aka ƙara wa masu gidajen karin watanni biyu bayan na farko domin ba su damar gyarawa ko sayar da gidajen ga wadanda za su iya kammalawa.
A cewar kwamishinan, gwamnati ta samar da muhimmman abubuwan more rayuwa kamar wutar lantarki daga cibiyar Tiga, ruwa, da tsaro, domin inganta yankunan.
Ya ƙara da cewa, gwamnati za ta duba yiwuwar mayar wa da masu gidajen da aka karɓe lasisin kuɗin da suka biya a baya, idan an tabbatar da cancantarsu.
Haka kuma, wadanda suka kai aikin gidansu tsakanin kashi 50 zuwa 95 cikin 100, an ba su wa’adin har zuwa 31 ga Disamba, 2025 don su kammala aikin.
Arch. Wudil ya tabbatar da cewa gidajen da suka koma karkashin gwamnati za a ci gaba da inganta su domin amfanin jama’a da ci gaban tattalin arzikin jihar, bisa tsarin adalcI, gaskiya da shugabanci nagari na gwamnatin Kano.