Babu bukatar yanke hukuncin kisa a Najeriya—Amnesty

0
7

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Dan Adam ta Duniya, Amnesty International, ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin Najeriya su soke hukuncin kisa daga tsarin dokokin ta.

Shugabar shirye-shiryen ƙungiyar a Najeriya, Barbara Magaji, ce ta bayyana hakan yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja, domin tunawa da Ranar Yaƙi da Hukuncin Kisa ta Duniya.

Taron dai ƙungiyar Amnesty International ta shirya shi ne tare da haɗin gwiwar Ofishin Jakadancin Faransa a Najeriya.

Magaji ta bukaci majalisar dokokin ƙasa da ta jihohi su cire duk wasu tanade-tanaden hukuncin kisa daga kundin tsarin mulki da dokokin da suka shafi manyan laifuka.

A cewarta, jihohi 26 da kuma birnin tarayya Abuja ne ke da dokokin da ke tanadar hukuncin kisa ga laifuka kamar garkuwa da mutane, fashi da makami, satar shanu, da tsafi.

Sai dai ta jaddada cewa, duk da waɗannan dokoki, ba a ga raguwar irin waɗannan laifukan ba, domin har yanzu ana samun ƙaruwa a aikata su a sassa daban-daban na ƙasar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here