Wani jami’in Kwastam ya mutu bayan kwana da ƴan mata uku a otal

0
10

An gano gawar wani jami’in Hukumar Kwastam da ake kira Lawal Tukur, wanda yake da mukamin Assistant Superintendent of Customs (ASC), a ɗaya daga cikin otel-otel na cikin garin Katsina a ranar Talata, 15 ga Oktoba, 2025.

Rahoton da wani mai binciken tsaro, Zagazola Makama, ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a Murjani Hotel, inda ma’aikatan otal ɗin suka same shi a mace da misalin ƙarfe 8:30 na safe.

Majiyoyi sun ce an gano kwanso na wasu sinadarai a kwandon shara da ke ɗakin. Rahoton ya kuma nuna cewa akwai mata uku da aka ce suna cikin otal ɗin a lokacin.

Wadanda aka ambata sun haɗa da:

Khadija Ali mai shekaru 34 daga unguwar Dutsin Amare,

Aisha Lawal mai shekaru 30 daga ƙaramar hukumar Ingawa,

da Hafsat Yusuf mai shekaru 22 daga unguwar Brigade a Kano.

An ce Khadija da Aisha sun kwana tare da jami’in a ɗakin, yayin da Hafsat ta iso daga baya ta kuma kwana a otal ɗin.

Jami’an otal ɗin sun sanar da hukumomi bayan gano gawar, kuma aka kai shi Asibitin FMC Katsina, inda likita ya tabbatar da rasuwarsa. An ajiye gawar a dakin ajiye gawa har sai an kammala binciken likita domin gano musabbabin mutuwar.

Hukumar Kwastam ta tabbatar da samun labarin kuma ta fara bincike kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here