Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA) ta bayyana cewa lafiyar Nnamdi Kanu ba ta kai ga barazana ga rayuwarsa ba, don haka yana da ƙoshin lafiya don ci gaba da fuskantar shari’a.
A ranar 26 ga Satumba, Mai shari’a James Omotosho ya umarci shugaban NMA da ya kafa tawagar bincike domin tantance halin lafiyar Kanu, don ganin ko yanayin sa na bukatar a fita dashi a duba lafiyar sa.
Wannan umarni na kotu ya biyo bayan buƙatar da aka shigar don a tura shugaban haramtacciyar ƙungiyar IPOB ɗin daga hannun hukumar DSS zuwa Asibitin Kasa da ke Abuja domin kula da lafiyarsa.