Ministan Ma’adinai, Dakta Dele Alake, ya bayyana cewa dole ne a rufe duk wata makaranta a Najeriya da ke karɓar kuɗin karatu da takardun kuɗin kasashen waje.
Ya yi wannan bayani ne a lokacin bikin Ranar hakar zinare ta Ƙasa da aka gudanar a Abuja yayin taron masu hakar ma’adinai na ƙasa karo na goma.
Alake ya ce wannan dabi’a ta karɓar kuɗin waje a cikin Najeriya wata hanya ce da ke rage darajar Naira da kuma janyo gibi a tattalin arziƙi.
> “Zan gabatar da shawara ga gwamnatin tarayya cewa a rufe dukkan makarantu da ke karɓar kuɗin karatu da ba na ƙasar nan ba. Wannan na cikin abubuwan da ke haifar da asara a tattalin arziƙinmu, amma mutane ba sa ganin muhimmancinsa,” in ji shi.