Gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da cibiyar samar da aikin yi ga matasa 

0
14
Tinubu
Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Shirin Cibiyar Samar da Ayyukan Yi ta Ƙasa domin haɗa matasa da damar samun aikin yi.

Ƙaramar ministar ƙwadago da ayyukan Yi, Nkeiruka Onyejeocha, ce ta bayyana haka a yayin wani taro da aka gudanar a birnin Legas, inda ta kuma ƙaddamar da Shirin Ayyuka da Ƙarfafa Ma’aikata da ake sa ran zai taimaka wajen samar da ayyuka sama da miliyan biyu da rabi (2.5) a kowace shekara.

Onyejeocha ta ce cibiyoyin za su taimaka wajen haɗa masu neman aiki da masu buƙatar ma’aikata ta hanyar amfani da fasahar zamani.

Ta yabawa gidauniyar Mastercard, bisa tallafin da take bayarwa wajen koyar da matasa sana’o’i da ƙwarewa, tare da kira ga gwamnati, kamfanoni da ƙungiyoyi su haɗa kai domin ƙarfafa samar da ayyukan yi a ƙasar nan.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here