Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za a fara ƙera fanel da sauran kayayyakin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a cikin jihar nan ba da jimawa ba.
Wannan mataki, a cewar gwamnatin, ya biyo bayan yarjejeniyar da aka kulla da kamfanonin Tricell Solar Solutions da IRS Green Energy, tare da haɗin gwiwar Hukumar Wutar Lantarki ta Karkara (REA) domin faɗaɗa samar da makamashi mai tsafta da sauki.
Mai magana da yawun Gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya bayyana cewa shugaban hukumar zuba jari ta jihar, Naziru Halliru, ne ya rattaba hannu kan yarjejeniyar a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf yayin taron Sabunta Makamashi na Najeriya (NERIF) 2025 da aka gudanar a Abuja.
Ya ce ƙulla wannan yarjejeniya na daga cikin muhimman matakan da gwamnatin Kano ke ɗauka domin bunƙasa masana’antu, ƙara samar da ayyukan yi, da kuma rage dogaro da makamashin wutar lantarki.
A cewar sanarwar, kamfanin IRS Green Energy zai gina masana’antar da za ta rika samar da 600 megawatts na kayayyakin hasken rana a shekara, yayin da Tricell Solar Solutions zai kafa mai ƙarfin 500 megawatts.