Rahotanni daga Jihar Filato sun tabbatar da cewa mutane 13, ciki har da matasa biyar, sun rasa rayukansu a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai a kauyen Rachas da Faan, da ke yankin Hyeipang, a Karamar Hukumar Barkin Ladi.
An ce maharan sun afka kauyukan ne da sassafe a ranar Talata, lokacin da mazauna garin ke barci, inda suka fara harbe-harbe ba gaira ba dalili.
Mai bai wa Gwamnan Jihar Filato shawara kan tsaro kuma kwamandan rundunar Operation Rainbow, Birgediya Janar Shippi Gakji (mai ritaya), ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya bayyana cewa:
> “Na ziyarci kauyukan da aka kai wa hari, kuma na halarci jana’izar wadanda aka kashe. Lamarin ya matukar tayar da hankali. Gwamnati na kan kokarin gano wadanda suka aikata wannan ta’asa domin a hukunta su.”
Shi ma shugaban Karamar Hukumar Barkin Ladi, Stephen Gyang Pwajok, ya tabbatar da faruwar lamarin tare da bayyana shi a matsayin aikata ta’addanci da rashin imani. Ya bukaci jami’an tsaro da su kara jajircewa wajen kamo masu hannu a kisan.
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa, rahoton kwamitin bincike kan tashin hankali da Gwamna Caleb Mutfwang ya kafa, ya bayyana cewa sama da mutane 11,000 ne suka rasa rayukansu a hare-haren da aka yi a Jihar Filato tun daga shekarar 2001 zuwa yanzu.
Gwamnatin jihar ta roki jama’a da su kwantar da hankulansu tare da bawa hukumomi hadin kai don ganin an samu zaman lafiya mai dorewa a yankin.