Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya nuna damuwarsa kan rahotannin da ke nuna bullar wani sabon reshen ƙungiyar Boko Haram a yankin Arewa ta Tsakiya.
A yayin zaman majalisar tsaron jihar da ya jagoranta, gwamnan ya bayyana cewa sabon ɓangaren ƙungiyar da ake kira “Wulowulo” ya fara nuna ayyukansa a wasu yankunan kusa da jihar, lamarin da ke iya zama barazana ga tsaron jihar.
“Sabuwar ƙungiyar Wulowulo, wadda ta ɓalle daga Boko Haram, ta fara bayyana a Arewa ta Tsakiya. Dole ne mu ɗauki matakan gaggawa don kare jiharmu daga shigowarsu,” in ji gwamnan.
Ya kuma umarci kwamishinan ‘yan sanda na jihar da daraktan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) su gudanar da bincike mai zurfi domin gano gaskiyar lamarin da kuma dakile yiwuwar barazanar tsaro.