Kungiyar shugabannin jihohin jam’iyyar PDP ta dakatar da shugabanninta biyu bisa zargin aikata abin da ya saba wa manufar jam’iyyar da kuma yunkurin lalata shirin babban taron gangamin jam’iyyar da ke tafe.
Wannan mataki na dakatarwar ya fito ne daga taron da shugabannin PDP na jihohi suka gudanar a ofishin jam’iyyar na Babban Birnin Tarayya Abuja, karkashin jagorancin sakataren rikon kwarya na kungiyar, Edward Percy Masha.
Shugabannin da abin ya shafa sun hada da Austine Nwachukwu na jihar Imo da kuma Amah Abraham Nnana na jihar Abia.
Kungiyar ta zargi shugabannin biyu da yin aiki tare da wasu “ƙungiyoyi na waje” da ake alakanta su da jam’iyyar APC, da nufin kawo cikas ga shirye-shiryen taron gangamin PDP da aka shirya gudanarwa a ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.