Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa yana sa ran jam’iyyar APC za ta mamaye jihohi 30 cikin 36 da ke ƙasar nan kafin shekarar 2026.
Idris ya bayyana hakan ne a lokacin taron dabarun aiki na watanni uku uku na shekarar 2025 na ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar APC wanda aka gudanar a Maiduguri, Jihar Borno.
Taron ya mayar da hankali ne kan yadda za a inganta haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin tarayya da jihohin da APC ke mulki.