Kotun tafi da gidan ka ta ɗaure ƴan kasuwa saboda rashin tsafta a Kano

0
10

Wata kotun tafi da gidanka a Jihar Kano ta yanke hukunci kan wasu mutane shida da aka kama suna aikata laifukan da suka shafi rashin tsafta a wajen kasuwancin su.

Mutanen sun shiga hannu ne bayan an same su da laifin rashin tsaftar kofar shaguna, kin samar da kwandon zubar da shara, zubar da shara a magudanan ruwa da kuma ajiye yashi, dutse da bulo a kan titin France Road da ke Sabon Gari a Kano.

Mai gabatar da kara, Barista Bahijja H. Aliyu, ta karanta musu tuhumar da ake yi, inda suka amsa laifinsu nan take.

Bayan sauraron karar, Mai Shari’a Halima Wali ta yanke musu hukuncin daurin sati biyu a gidan gyaran hali ko biyan tarar Naira 200,000 kowannen su.

Tun da farko, Hukumar kwashe shara da tsaftar muhalli ta Jihar Kano ta riga ta yi musu gargadi tare da ba su umarnin gyara wuraren nasu da kuma kwashe kayan ginin da suka zubar a kan hanya amma suka bijirewa amincewa da gargaɗin.

Kotun ta bayyana cewa halin da suka nuna ya saba wa dokokin tsaftar muhalli, don haka ta tabbatar da laifin da ake tuhumarsu da shi, wanda ya haɗa da:

Rashin tsafta

Rashin samar da kwandon shara

Zubar da shara a magudanan ruwa

Ajiye yashi, dutse da bulo a kan titi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here