Babbar Kotun Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Musa Dahiru Muhammad, ta yanke wa wani mai horas da ƙungiyar ƙwallon ƙafa, Hayatu Muhammad, hukuncin ɗaurin shekaru takwas a gidan yari ba tare da zaɓin biyan tara ba, bisa laifin yin luwadi da ƙaramin ɗan wasan sa.
Wannan hukunci ya biyo bayan tabbatar da cewa wanda ake tuhuma, mazaunin unguwar Sanka a Kano, ya aikata laifin sau biyu a wurare daban-daban.
A zaman kotun, Hayatu ya ƙi amincewa da tuhumar da ake masa. Sai dai lauyan gwamnati na Kano, Barrista Ibrahim Arif Garba, ya gabatar da shaidu biyar waɗanda suka tabbatar da zargin a gaban kotu. Shi kuwa wanda ake tuhuma, shi kaɗai ne ya tsaya a matsayin shaida wajen kare kansa.
Kotun ta tabbatar da cewa an karya sashe na 284 na Dokar Penal Code, wanda ke hukunta irin wannan laifi.
Bayan nazarin bayanan shaidu da hujjojin da aka gabatar, Mai Shari’a Dahiru, ya bayyana cewa an tabbatar da laifin ba tare da wata shakka ba.
Daga nan sai ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru huɗu kan kowane daga cikin tuhume-tuhumen biyu, tare da umartar a gudanar da hukuncin biyun lokaci guda, daga ranar da aka yanke hukuncin.