Hukuma ta tabbatar da sauya wurin tsare Malam Abduljabbar

0
12

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa sauya wurin da ake tsare da Malam Abduljabbar Nasiru Kabara zuwa wani ɗaya daga cikin cibiyoyin gyaran hali da ke ƙarƙashin gwamnatin tarayya ba wata matsala bace, illa dai wani tsarin gudanarwa na yau da kullum bisa ga doka da tsarin aikin hukumar.

A cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar, CSC Musbahu Lawan K/Nassarawa ya fitar, hukumar ta ce sauya wurin ɗaure wani fursuna zuwa wata cibiya daban abu ne da aka tanada a cikin dokar Nigerian Correctional Service Act, 2019, domin kyautata gudanar da ayyuka da tabbatar da tsaro da ingantaccen kulawa ga fursunoni.

Hukumar ta ce irin waɗannan matakai na sauya fursunoni ana ɗaukar su ne bisa dalilai na tsaro, irin nau’in laifi, da kuma bukatun gyara da sake tarbiyya na mutum.

Ya kuma tabbatar da cewa dukkan hakkoki da walwalar Malam Abduljabbar suna nan daram, tare da tabbatar da cewa canjin bai shafi matsayinsa na doka ko damar samun lauyoyinsa ba.

Hukumar ta jaddada aniyarta na ci gaba da tabbatar da tsaro, gyara da sake shigar da fursunoni cikin al’umma bisa tsarin da doka ta tanada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here