Gwamnan Bayelsa Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

0
7

Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar PDP.

Mai magana da yawunsa, Daniel Alabrah, ne ya tabbatar da hakan ta wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.

A cewar Alabrah, gwamnan ya fice daga jam’iyyar tare da Kakakin Majalisar Dokokin jihar, Rt. Hon. Abraham Ingobere, da kuma dukkan ‘yan majalisar jihar da ke karkashin jam’iyyar PDP.

Rahotanni sun nuna cewa wannan matakin ya kawo karshen jita-jitar da ake ta yadawa cewa Diri na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, duk da cewa ba a bayyana jam’iyyar da zai koma ba.

Majiyoyi sun ce Diri ya sanar da ficewarsa ne yayin taron majalisar zartarwa ta jihar da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Yenagoa, inda kuma aka tabbatar da cewa ya miƙa takardar ajiye mukaminsa ga jam’iyyar PDP.

Har ila yau, akwai rahotanni cewa wasu mambobin majalisar zartarwar jihar ma sun bi sahunsa wajen yin murabus.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here