Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa babu wani ɗan siyasa a Najeriya da zai iya kalubalantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Mai ba Shugaban Kasa shawara kan sadarwar manufofi, Daniel Bwala, ne ya bayyana haka a wani taro da aka yi da kungiyoyi masu goyon bayan Tinubu a Abuja.
Bwala ya ce nasarorin da gwamnatin Tinubu ta samu a fannin tattalin arziki, noma, tsaro da aikin yi sun tabbatar da cewa shugaban zai sake samun nasara a zabe mai zuwa.
Ya kara da cewa gwamnati na shirin gudanar da taruka a Birtaniya, Amurka da Kanada domin hada kai da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje.
A nasa bangaren, tsohon dan majalisar tarayya, Hon. Ehiozuwa Johnson Agbonayinma, ya ce Shugaba Tinubu ya gina tubalin ci gaba mai dorewa, yana mai cewa “a 2027 babu makawa zai sake lashe zabe.”


