Ana yunƙurin ɗauke makarantar CAS daga garin mu–Al’ummar Minjibir

0
15

Wasu kungiyoyi a karamar hukumar Minjibir tare da ƙungiyoyin ɗalibai na yankin sun gudanar da zanga-zangar lumana don nuna adawa da zargin da suke yi na makarantar CAS daga garin Minjibir.

A cewar masu zanga-zangar, mutanen Minjibir ne suka yi gagarumin kokari wajen kawo makarantar zuwa yankin domin sauƙaƙa wa al’ummar su wajen samun ilimi. Sai dai yanzu suna zargin cewa ana shirin canja mata matsuguni zuwa wani wuri daban, abin da suka ce ba za su yarda da shi ba.

Shugaban gamayyar ƙungiyoyin, Malam Hassan Bello Minjibir, ya bayyana cewa manufar zanga-zangar ita ce neman gwamnati ta dakatar da wannan shiri.

Haka kuma, ɗaliban makarantar maza da mata sun roƙi Gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya shigo cikin lamarin domin ceto makarantar daga wannan hali.

A nasa ɓangaren, Comrade Nasiru Yusuf, shugaban ƙungiyar ɗaliban makarantar, ya bayyana cewa sama da ɗalibai 1000 ke karatu a makarantar, wanda da yawan su mata ne, ciki har da iyaye mata masu neman ilimi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here