Yayin da damina ke gab da karewa, manoma da dama a karamar hukumar Shinkafi ta jihar Zamfara na fargabar yadda za su girbe amfanin gonarsu sakamakon hare-haren ƴan bindiga da ke addabar yankin.
Rahotanni sun nuna cewa ƴan bindigar na kai farmaki garuruwa, suna sace dabbobi da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, abin da ya sa yawancin manoma ba sa iya zuwa gonakinsu.
Wani mazaunin yankin ya shaida cewa:
> “Amfanin gona ya girma, amma babu wanda ke iya zuwa ya ɗebe. Idan ka je, za su kama ka su tafi da kai daji su nemi kuɗin fansa. Kuɗin da suke nema ma, yafi abin da manomi zai samu daga gonarsa.”
Ya ƙara da cewa lamarin ya yi kamari a garuruwan Birnin Yero, Jangeru, Shanawa da Shinkafi kanta, inda a kowace rana ake samun hare-hare da sace mutane.
Saboda tsoron faɗa wa hannun ƴan bindiga, wasu manoma yanzu sun koma bin dare domin shiga gonaki su samo abin da za su ci.
Daga nata ɓangaren, gwamnatin Zamfara ta ce tana sane da halin da jama’ar yankin ke ciki. Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan kafafen yaɗa labarai, Mustafa Jafaru Kaura, ya bayyana cewa gwamnati tana ɗaukar matakan tsaro don dawo da zaman lafiya.
#Zamfara #Shinkafi #Tsaro #Manoma #YanBindiga #Noma #Nigeria