‘Yan majalisar wakilai uku sun fice daga jam’iyyar PDP zuwa APC

0
7

Wasu ‘yan majalisar wakilai uku daga jihar Kaduna sun sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC a zaman majalisar da aka gudanar ranar Talata.

Wadannan ‘yan majalisar sun hada da Aliyu Abdullahi (mai wakiltar mazabar Ikara/Kubau), Abdulkareem Ahmed (Kaduna ta kudu), da Sadiq Abdullahi (Sabon Gari).

Mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu, ne ya karanta takardun sauya shekar tasu yayin zaman.

Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya halarci zaman majalisar domin ganawa da ‘yan majalisar yayin da suke bayyana sauya shekar.

‘Yan majalisar sun ce rikicin cikin gida da ke damun jam’iyyar PDP ne ya sa suka yanke shawarar komawa APC.

Sai dai Kingsley Chinda, shugaban marasa rinjaye a majalisar, ya kalubalanci wannan mataki, yana mai cewa babu wani rarrabuwar kai a jam’iyyar da zai ba su damar yin hakan bisa doka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here