Sojoji sun ƙwace mulkin ƙasar Madagascar 

0
19

Rundunar sojin Madagascar ta sanar da karɓe ragamar mulkin ƙasar, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tabbatar.

Haka zalika, kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa wani soja mai mukamin Kanal ya tabbatar da faruwar juyin mulkin.

Kanal Michael Randrianirina, shugaban rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa, ne ya karanta sanarwar a gidan rediyon ƙasar, inda ya ce: “Tun daga yau, rundunar soji ta karɓi mulkin wannan ƙasa.”

Rahotanni sun nuna cewa a ƙarshen mako ne dakarun tsaron fadar shugaban ƙasar suka nuna rashin goyon bayansu ga shugaban ƙasa, tare da shiga zanga-zangar masu neman ya sauka daga mulki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here