Shugabar riƙon INEC ta fara ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa

0
9

Shugabar riƙon INEC ta fara ganawa da shugabannin jam’iyyun siyasa

Mai riƙon Shugabancin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC), May Agbamuche-Mbu, ta gudanar da taron farko da shugabanni da sakatarorin jam’iyyun siyasa a babban ofishin hukumar da ke Abuja a ranar Talata.

Rahotanni sun bayyana cewa ganawar ta zama wani ɓangare na shirin hukumar na tattaunawa da masu ruwa da tsaki kafin zaɓen gwamnan Anambra da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba.

Duk da cewa cikakken bayani game da abin da aka tattauna a taron bai fito, majiyoyi sun ce taron ya mayar da hankali ne kan gyara al’amuran shirye-shirye da daidaita tsarin gudanar da zaɓe yadda za a tabbatar da sahihancin sakamako.

Wannan shi ne karo na farko da Agbamuche-Mbu ke jagorantar irin wannan zama tun bayan karɓar mukami daga Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 7 ga Oktoba.

Yakubu ya sauka daga mukaminsa bisa tanadin sashi na 306 na kundin tsarin mulkin Najeriya, yayin da Majalisar Kasa ke jiran tabbatar da Farfesa Joash Ojo Amupitan a matsayin sabon shugaban hukumar bayan naɗin da Tinubu, ya yi masa.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here