Jam’iyyar PDP ta sanar da dage babban taron kwamitin zartarwarta da aka shirya gudanarwa a ranar Laraba, 15 ga Oktoba, 2025.
A cewar wata sanarwa da jam’iyyar ta wallafa a shafinta na X, tace an ɗauki wannan mataki ne bayan wani taron gaggawa da kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya gudanar a Abuja a ranar Litinin.
Jam’iyyar ta bayyana cewa za ta sanar da sabuwar rana a nan gaba, tare da roƙon mambobinta da su jira sabon jadawalin taron.
PDP na fuskantar ƙalubale a cikin gida sakamakon yawaitar ficewar manyan mambobinta zuwa jam’iyyar APC mai mulki, ciki har da jita-jitar cewa wasu daga cikin gwamnoninta biyu ma na shirin komawa APC.