Babbar Kotun Jihar Kano mai lamba ɗaya, karkashin jagorancin Mai Shari’a Dije Abdu Aboki, ta tura wani matashi mai suna Abubakar Hudu zuwa gidan gyaran hali bisa zargin yunkurin aikata kisan kai.
Ana tuhumar Abubakar Hudu da yunkurin kashe wani mutum mai suna Abdulsalam Ahmad, inda ake zarginsa da jikkata shi ta hanyar amfani da makami mai haɗari, wanda ya bar masa raunuka a kai da hannaye.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar 9 ga watan Satumba, 2024, da misalin karfe 7:00 na dare, a unguwar Kurna dake cikin birnin Kano.
A zaman kotun, Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Barista Abdulkareem Kabir Maude, wanda ya wakilci gwamnatin jiha, ya gabatar da ƙarar tare da neman a karanta tuhumar ga wanda ake zargi.
An karanta masa tuhumar, amma Abubakar Hudu ya musanta aikata laifin. Lauyansa, Barista Ibrahim Mu’az, ya bayyana cewa sun shirya tsaf don kare kansu a gaban kotu.
Masu gabatar da ƙara sun nemi kotu ta ba su lokaci domin gabatar da shedunsu uku (3).
Mai Shari’a Dije Abdu Aboki ta amince da buƙatar, inda ta dage shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Nuwamba, 2025 domin cigaba da sauraron karar.