Kotun jihar Kano ta bada umarnin a tura wani mai gidan marayu a Asaba, Ogugua Christopher, zuwa gidan gyaran hali bisa tuhumar da ake yi masa ta sace wa da safarar yara daga Kano zuwa jihar Delta.
An gurfanar da Christopher tare da wasu mata biyu, Hauwa Abubakar da Nkechi Odlyne, bisa tuhuma 15 da suka haɗa da yin makirci da satar yara, wanda ya saba da sashe na 97 da 273 na kundin dokokin laifuka na jihar Kano, da kuma sashe na 32(5) na dokar kula da yara da matasa.
Masu gabatar da ƙara sun ce daga watan Yuni 2016 zuwa Disamba 2021, waɗannan mutanen sun haɗa baki wajen satar yara daga Kano da kuma sayar da su a jihar Delta.