Gwamnatin tarayya ta sauya tsarin samun gurbin karatu a gaba a makarantun sakandire 

0
9

Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya ta sanar cewa daga yanzu, ɗaliban da ke neman shiga jami’a ko kwalejojin fasaha a fannin Arts ba lallai ne su samu “credit” a lissafi (Mathematics) ba kafin su samu gurbin karatu.

Ministan Ilimi, Dr. Maruf Tunji Alausa, ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin kaddamar da sabbin ka’idojin shigar jami’a da makarantun gaba da sakandare a Abuja.

> “An sabunta ƙa’idojin domin kawar da shingayen da ke hana ɗalibai samun gurbin karatu ba tare da rage ingancin ilimi ba,” in ji ma’aikatar a cikin sanarwar da ta fitar.

A cewar sabon tsarin:

Jami’o’i: Ana buƙatar aƙalla credits 5, ciki har da Turanci (English), yayin da Lissafi zai zama dole ne kawai ga fannoni na Kimiyya, Fasaha da Zamantakewa.

Polytechnic (ND): Ana buƙatar credits 4 – Turanci dole ne ga fannoni da ba kimiyya ba, yayin da Lissafi ke zama dole ga na kimiyya.

Polytechnic (HND): Credits 5 ciki har da Turanci da Lissafi.

Colleges of Education (NCE): Credits 4 – Turanci dole ga Arts da Social Sciences, yayin da Lissafi ya zama wajibi ga Kimiyya da Fasaha.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here