Gwamnan Enugu Peter Mbah ya koma jam’iyyar APC

0
7

Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah, ya fice daga jam’iyyar PDP inda ya koma jam’iyyar APC.

Mbah ya bayyana matakin ne a yau Talata yayin wani taron manema labarai da ya kira, inda ya ce ya dauki wannan mataki domin inganta ayyukan ci gaban jihar da kuma daidaita kansa da manufofin jam’iyyar APC wajen kawo cigaba da bunƙasa tattalin arziki.

Gwamnan ya ce manufarsa ita ce ci gaba da kare muradun jama’ar Enugu, tare da fatan cewa tafiyarsa da APC za ta kawo ƙarin dama ta haɗin kai da cigaba a jihar.

Ya kuma gode wa tsohuwar jam’iyyarsa PDP bisa goyon bayan da ta ba shi tsawon shekaru, yana mai cewa wannan sauyi wajibi ne don cimma manyan manufofin gwamnatinsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here