Mahukunta sun sauya wurin da ake tsare da Malam Abduljabbar Sheikh Nasiru Kabara daga gidan gyaran hali na Kurmawa zuwa wani wuri na daban, bayan da rahotanni suka nuna cewa wasu daga cikin magoya bayansa sun fara yin barazana da cewa za su kai hari domin ceto shi.
Wani rahoto daga shafin daliban Malam Abduljabbar da kuma kaninsa, Askiya Nasiru Kabara, sun bayyana cewa an dauki wannan mataki ne bayan da magoya bayan malamin suka bayar da wa’adin kwanaki don a sako shi, ko kuma su je da kansu su fitar da shi daga gidan gyaran hali.
A cewar su, an kai wa Abduljabbar abincinsa da safe kamar yadda aka saba, amma daga baya suka samu labarin cewa an tura shi wani wuri daban saboda dalilai na tsaro.
Abduljabbar Nasiru Kabara yana tsare tun lokacin da kotun shari’ar musulunci karkashin jagorancin Alkali Ibrahim Sarki Yola ta same shi da laifin batanci ga Annabi Muhammad (SAW), tare da yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Zuwa yanzu dai ba’a ji Æ™arin haske daga mahukunta ba.