Fitaccen malamin addinin Musulunci, Farfesa Mansur Ibrahim Sakkwato, ya bayyana rashin amincewarsa da afuwar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa wasu masu manyan laifuka, ciki har da masu kisa da masu safarar miyagun ƙwayoyi.
Farfesan ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya ce babu wani ɗan adam da ke da ikon yafe laifin da ya shafi hakkin wani mutum, domin irin waɗannan laifuffuka Allah ne kaɗai Ya ke da ikon yafe su.
“Babu wanda yake da ikon yafewa wanda ya karya dokokin Allah. Duk wanda ya yi hakan, ya aikata zalunci,” in ji Farfesa Mansur.
Ya yi nuni da hadisin Annabi Muhammadu (S.A.W.) wanda ya ce:
“Na rantse da Allah, da Fatima ‘yar Muhammadu za ta yi sata, da na yanke mata hannu.”
Farfesan ya ce wannan hadisin na nuna cewa adalcin Musulunci bai da bambanci tsakanin mai ƙarfi da mara ƙarfi, ko mai mulki da talaka.
Ya ƙara da cewa, duk wanda ya yafe laifin da ya shafi hakkin wani, ya tsallake iyakar da Allah Ya shimfiɗa, yana kuma nuna zalunci ga al’umma.
Idan za’a iya tunawa afarkon makon da ya gabata ne Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanar da yafe wa mutane 175, ciki har da wadanda aka taɓa yankewa hukuncin kisa saboda laifin kisa ko safarar kwaya, damfara, cin hanci, garkuwa da mutane da dai sauransu.

