‘Yan bindiga sun sace ɗan jaridar PRNigeria 

0
62

Rahotanni sun tabbatar da cewa an sace wani ɗan jarida mai suna Salis Manaja, wanda ke aiki da kamfanin Image Merchants Promotion Limited (IMPR), masu wallafa jaridun PRNigeria da Economic Confidential.

Manaja yana kan hanyarsa daga Abakaliki, Jihar Ebonyi, zuwa Ilorin, Jihar Kwara, domin halartar shirin shekara-shekara na horar da matasan ƴan jarida wanda PRNigeria, ke shirya wa.

Wata majiya daga abokansa ta bayyana cewa masu garkuwar sun tuntubi iyalansa, inda suka nemi kuɗin fansa, sai dai ba a bayyana adadin kudin da suka nema ba.

Shugaban shirin, Muhammad Dahiru Lawal, ya ce duk ƙoƙarin da abokansa suka yi don su same shi ta waya abin ya ci tura, domin layinsa ya daina shiga.

Har yanzu ba a tabbatar da ainihin wurin da aka yi garkuwar dashi ba, yayin da hukumomin tsaro ke cigaba da bincike.

Shirin PRNigeria Young Communication Fellowship shiri ne da ake gudanarwa a Kano, Abuja, da Ilorin domin koyar da matasan ‘yan jarida dabarun aikin jarida da sadarwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here