Sojan Najeriya Ya Kashe Matar sa Ya Kashe Kansa a Bariki

0
47

Rundunar Sojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani jami’in ta, mai suna Akenleye Femi, wanda ake zargin ya kashe matarsa sannan ya kashe kansa a barikin Wawa da ke jihar Neja.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 11 ga Oktoba, 2025, inda ya jefa mazauna barikin cikin tashin hankali da mamaki kan abin da ya iya haifar da hakan.

Mai rikon mukamin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Soji ta 22, kaftin Stephen Nwankwo, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa marigayin yana aiki a bataliya ta 221 da ke barikin Wawa kafin rasuwarsa.

Rundunar ta ce ana ci gaba da bincike domin gano ainihin abin da ya haddasa wannan mummunan lamari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here