Kungiyar Lauyoyin Yan Asalin Jihar Kano ta sake neman kasashen duniya da su shiga cikin batun zargin kisan mutane da ake yiwa dan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa da Tudun Wada, Hon. Alhassan Ado Doguwa, a lokacin zaben 2023.
Kungiyar ta aika da takardu da hotuna zuwa ofisoshin jakadancin kasashen Amurka, Birtaniya, Saudiyya, da Majalisar Dinkin Duniya, tana neman a gudanar da cikakken bincike da daukar matakin shari’a domin tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.
Haka kuma, a baya kungiyar ta kai irin wannan korafi zuwa ofishin Kwamishinan Shari’a na Kano da Majalisar Tarayya, tana jaddada bukatar gwamnati da hukumomi su tabbatar da adalci a lamarin.