Hisbah ta Kano ta kama matasa 5 da suka ɗaura aure babu amincewar iyaye

0
16
Hisbah
Hisbah

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta kama matasa biyar bisa zargin gudanar da aure ba tare da samun izinin iyaye ko bin tsarin shari’a ba.

Mataimakin kwamandan hukumar, Dakta Mujahideen Aminuddeen, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Litinin a Kano.

Ya ce wadanda aka kama sun haɗa da ango, amarya da wasu mutum uku da suka tsaya matsayin wakilai da shaida a wajen daura auren.

A cewar Aminuddeen, an gudanar da auren ne da sadaki na naira 10,000 kacal wanda yake ƙasa da mafi ƙarancin sadaki da shari’ar Musulunci ta tanada.

Ya ƙara da cewa wannan auren ya sabawa tsarin Musulunci da kuma dokokin da suka shafi aure.

 Hakan ya sa Hisbah ta kaddamar da bincike don gano cikakken abin da ya faru.

Dr. Aminuddeen ya yi kira ga iyaye da su kula da harkokin ’ya’yansu, musamman a lamurran da suka shafi aure, domin kare su daga fadawa cikin irin wannan kuskure.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here