Gwamnatin Tarayya ta bukaci kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa, ASUU, da ta dakatar da yajin aikin gargadi da ta fara, tana mai cewa ta cika duk bukatun da kungiyar ta nema.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan a tattaunawar sa da tashar talabijin ta Channels, inda ya ce gwamnatin ta tattauna da ASUU sau da dama tun bayan shigar sa ofis, kuma babu dalilin cigaba da yajin aikin.
Alausa ya ce, “Mun biya duk abin da ASUU ta nema, don haka babu huja ko dalilin ci gaba da yajin aiki. Muna rokon su da su koma bakin aiki.”
Sai dai a ranar Lahadi, shugaban ƙungiyar ASUU, Farfesa Chris Piwuna, ya sanar da fara yajin aikin gargadi na makonni biyu saboda gwamnatin ta kasa aiwatar da alkawurran da ta dauka.
Yajin aikin na zuwa ne bayan cikar wa’adin kwanaki 14 da ASUU ta bai wa gwamnati tun ranar 28 ga Satumba, 2025.