Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Najeriya (ASUU) ta kaddamar da yajin aikin gargaɗi na tsawon makonni biyu, bayan cikar wa’adin da ta bai wa gwamnatin tarayya don magance matsalolin da suka shafi walwalar malamai da ingancin jami’o’i.
Shugaban ƙungiyar, Farfesa Chris Piwuna, ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a Jami’ar Abuja, inda ya ce ASUU ta ɗauki wannan mataki ne bayan wa’adin kwanaki 14 da ta bai wa gwamnati tun daga ranar 28 ga Satumba ya ƙare ba tare da an aiwatar da komai ba.
> “Daga safiyar Litinin, 13 ga Oktoba, 2025, dukkan rassan ASUU za su janye daga gudanar da duk wani aiki. Wannan yajin aiki na gargadi zai shafi dukkan ayyukan da malaman jami’a ke yi,” in ji Farfesa Piwuna.
Ƙungiyar ta zargi gwamnati da sakaci wajen bin yarjejeniyar da ke tsakaninsu da kuma nuna halin ko-in-kula wajen tattaunawar da ake yi domin magance matsalolin da suka daɗe suna addabar jami’o’i.
Sai dai a martanin da ta fitar, gwamnatin tarayya ta gargadi malaman da suka shiga yajin aikin cewa za ta aiwatar da tsarin “ba aiki, babu albashi.”
Kakakin Ma’aikatar Ilimi, Folasade Boriowo, ta bayyana cewa gwamnati ta yi wa ASUU tayin da ya ƙunshi matakai masu muhimmanci na gyara, ciki har da inganta yanayin aiki, kula da walwalar malamai don ingantaccen gudanarwar jami’o’i.
Ta ce duk da waɗannan matakai, ƙungiyar ASUU ta ƙi bayar da haɗin kai, abin da ta ce na iya jefa harkar ilimi cikin wani hali.