Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 236 a jihohi 27 da Abuja — NEMA

0
17

Hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) ta bayyana cewa mutane 236 ne suka rasa rayukansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta addabi jihohi 27 da Babban Birnin Tarayya Abuja a bana.

Rahoton hukumar ya nuna cewa sama da mutane 409,000 ambaliyar ta shafa, inda fiye da 135,000 suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana cewa sun ɓace, kuma 826 sun ji rauni.

Jihar Niger ce ta fi fuskantar asarar rayuka inda mutum 163 suka mutu, sai Adamawa da mutum 59, yayin da jihohin Taraba, Sokoto, Jigawa, Yobe, Gombe, da Borno ma suka bayar da rahoton mutuwar wasu mutane.

Haka kuma, ambaliyar ta lalata gidaje 47,708 da gonaki 62,653 a sassa daban-daban. NEMA ta ce cikin waɗanda suka fi shan wahala akwai mata 125,000, yara 188,000, da tsofaffi 18,000.

Hukumar ta tabbatar da cewa tana ci gaba da sa ido kan lamarin tare da haɗa kai da gwamnatocin jihohi da kungiyoyin agaji domin taimaka wa waɗanda abin ya shafa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here