Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya sanar da kawo ƙarshen yaƙin da aka dade ana gwabzawa a Gaza, wanda ya kai tsawon shekaru biyu.
Yayin da yake jawabi a gaban majalisar dokokin ƙasar tare da halartar shugaban Amurka, Donald Trump, Netanyahu ya ce: “A yau kalandar Yahudawa ta nuna ƙarshen yaƙin da muka shafe shekaru biyu muna yi.”
Ya kuma bayyana godiya ga sojojin Isra’ila da suka rasu ko suka jikkata a lokacin rikicin, inda ya ambaci wasu daga cikin sunayensu.
Netanyahu ya kara da cewa, “Jajircewar waɗannan gwarazan ce ta tabbatar da dorewar Isra’ila.
A yayin yaƙin dai an kashe dubban falasɗinawa mafi yawan su mata da ƙananun yara, baya ga rushe musu gidaje da sauran wajen gudanar da rayuwar yau da kullum.