Tinubu zai tafi ƙasar Italiya don halartar taron tsaron ƙasashen Afrika

0
26

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai tafi Rome, babban birnin ƙasar Italiya, a yau Lahadi domin halartar wani taron da zai mayar da hankali kan batun tsaro a yankin Afirka ta Yamma.

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, an bayyana cewa taron zai fara ne ranar Litinin, 14 ga watan Oktoba, tare da haɗa shugabanni da manyan hafsoshin tsaro daga sassa daban-daban na Afirka domin tattauna hanyoyin magance ƙalubalen tsaro da ke addabar yankin.

An fara gudanar da taron a shekarar 2015 ƙarƙashin jagorancin Sarkin Jordan, Abdullah II, tare da haɗin gwiwar gwamnatin Italiya, da nufin ƙarfafa haɗin kai a yaƙin da ake yi da ta’addanci da ƙungiyoyin masu tayar da hankali.

Fadar shugaban ƙasa ta ce Tinubu zai yi ganawa ta musamman da wasu shugabannin ƙasashe a gefen taron domin lalubo sabbin hanyoyin da za su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalolin tsaro a Afirka ta Yamma.

A cikin tawagar da ke rakiyar shugaban akwai Ministan Tsaro, Badaru Abubakar, Ƙaramar Ministar Harkokin Waje, Bianca Ojukwu, Mai Ba da Shawara kan Tsaro, Nuhu Ribadu, da Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri (NIA), Mohammed Mohammed.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here